Kaduna 2023: ISAH ASHIRU YA GABATAR DA KUDURORI 5 DA ZAI AIWATAR DOMIN BUNKASA JIHAR KADUNA IN AN ZABE SHI GWAMNA

Daga Balarabe Junaidu Nuhu, Kaduna.

Dan takarar kujerar gwamna a Jihar Kaduna a karkashin tutar Jam’iyyar PDP Honorabul Isah Muhammad Ashiru, ya gabatar da kundin kudurori 5 wanda in aka zabe shi a matsayin gwamnan Jihar zai aiwatar da nufin bunkasa ci gaban Jihar tare da inganta rayuwar al’amura baki daya.

Honourable Isah Muhammad Ashiru ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai wanda ya gudana a cibiyar kungiyar ‘yan Jaridu NUJ reshen Jihar Kaduna a yau laraba.

Kudurorin guda biyar su ne, Ilimi, Noma. Tsaro, Kiwon lafiya, da samar da aikin ga mata da matasa.

A batun tsaro, ya nuna taikaicin shi a game halin da Jihar Kaduna ta tsinci kan ta na tabarbarewar rashin tsaro wanda ya ce, ya haifar da koma baya a game bunkasar Jihar, sa’annan al’amurar Jihar ba su cikin natsuwa.

Ya ce alhakin gwamnati ne kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya bayar wanda aka yi mashi gyara na 1999 ta kare rayuka da dukiyoyin al’amurar Jihar su sami natsuwa inda ya ce in an zabe shi zai magance yawaitar rashin tsaro a Jihar Kaduna.

Honourable Isah Muhammad Ashiru da ya juya a game sha’anin noma, ya abin takaici ne ace buhun takin zamani ya kai naira 35,000 a yayin da kudin buhun Masara ko Gero bai wuce naira 22,000, wanda sai manomi ya sayar da buhu daya na Masara ko Gero sa’annan zai yi dan ciko ya iya sayen buhun takin zamani guda daya, wannan ya ce za su gyara wannan domin noma ya inganta, manoma su sami sauki, abinci ya yawaita.

Ya kara da cewa in an zabe su za su bullo da sabbin dabaru na bunkasa noma na zamani wanda za a Samar wa matasa aikin ta fannin noma tare da samar da daukakin abin da ya shafi abubuwan da za su bunkasa noma, kamar magungunan kashe kwari masu lalara amfanin gona, da kuma dukkan na’urorin da ake amfani da su domin inganta noma.

Haka ya ce gwamnatin shi za ta kafa kananan masana’antu domin sarrafa amfanin gona kamar Masara, Tumatir da Chitta wanda za su Samar wa dubban matasa aikin yi.

Honourable Isah Muhammad Ashiru ya ce muddin ba a samar wa matasa ba da aikin yi, to kuwa zai samo wa kan shi aikin yi wala ta ingantaccen hanya ne, kuwa akasin haka wanda a Karshe kowa zai shafa.

Dan takarar kujerar gwamnan Jihar Kaduna a karkashin tutar Jam’iyyar PDP har ila yau ya ce sha’anin Ilimi ya tabarbare dalili kuwa shi ne cire tallafin da gwamnati mai mulkin Jihar ta kuma ta tsauwala kudin makaranta ta yadda wasu iyayen sun kasa biyan kudin karatun ‘ya’yan su, musamman wadanda ke karatu a Jami’ar Jihar Kaduna, wannan ya ce za su magance wannan matsalar.

Da ya juya kan batun Kiwon lafiya, Isah Muhammad Ashiru ya ce al’amuran Kiwon lafiya ya tabarbare a asibitoci domin akasarin masu zuwa neman magani ba sa iya biyan kudaden da ake cewa su biya na magani, haka wasu asibitocin babu wadatattun kayan aiki inda ya ce za su magance wannan matsalar da zarar an zabe su.

Ta bangsren makarantun koyar da sana’o’i kuwa wato BATC wanda ya ce ana da guda ashirin da uku ne a Jihar Kaduna amma a yanzu guda sha bakwai ne kawai ke aiki inda ya ce za su gyara su zuba duk kayakin da ake bukata na koyarwa.

Ya ce in aka gyara su, za a rika yaye matasa masu sana’o’i iri daban dabam wanda zai kawar da zaman banza a tsakanin su, yawaitar aikata munanan dabi’u a tsakanin matasa zai ragu, zaman lafiya zai inganta, Jihar ta sami ci gaba.

Isah Ashiru haka da ya koma kan kungiyar’yan Jaridu kuwa, ya ce aikin su na da mahimmanci a tsakanin al’umma da mahukunta don haka ya ce, zasu yi aiki kafada da kafada da su.

Da yake gabatar da jawabin shi, Daraktan Janaral na yakin neman zaben Honorabul Isah Muhammad Ashiru, Alhaji Haruna Sa’id AG, ya ce suna bukatar hadin kan kungiyar ‘yan Jaridu domin nuna wa Al’amurar Jihar Kaduna irin tanadin da suka yi domin ciyar da Jihar Kaduna gaba.

Tun da farko a jawabin ta, shugabar kungiyar’yan Jaridu NUJ reshen Jihar Kaduna, Hajiya Asma’u Yawo Halilu, ta yi wa Dan takarar kujerar gwamnan Jihar Kaduna a karkashin tutar Jam’iyyar PDP, Isah Muhammad Ashiru da mataimakin shi tare da tawagar shi barka da zuw cibiyar inda ta tabbatar masu da cewa su kungiyar ‘yan Jaridu NUJ, za su yi aikin su bisa kan bin dokokin aikin su na watsa labarai inda ba za su fifita wani dan takara ba a kan wani, kowane zai zo ya bayyana irin tsarin da ya shirya domin aiwatarwa in an zabe shi a matsayin gwamnan Jihar Kaduna.

Daga Karshe, mukadsashin shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna Mista Hassan Hyat, wato Honorabul Ibrahim Lawal Nuhu Kayarda, ya nuna godiya da wannan damar da kungiyar’yan Jaridu NUJ ta ba su inda su ka zo da dan takarar su na Jam’iyyar PDP Isah Muhammad Ashiru wanda ya gabatar da kundin kudurorin shi guda biyar ga al’amurar Jihar Kaduna domin aiwatar da su don kawo gyara a kan abubuwan da suka tabarbare wanda hakan ya haifar da koma baya ga ci gaban Jihar Kaduna.

Daga Karshe, Honourable Isah Muhammad Ashiru ya mika wa shugabar kungiyar’yan Jaridu NUJ reshen Jihar Kaduna,Hajiya Asma’u Yawo Halilu kwafen kundin tsarin kudurorin biyar wadanda ya ke son ya aiwatar in an zabe shi a matsayin gwamnan Jihar Kaduna.

Dan takarar kujerar gwamnan a karkashin tutar Jam’iyyar PDP, Isah Ashiru ya ci gaba da cewa gwamnatin shi idan aka zabe shi zai mayar da hankalin shi wajen kyautata rayuwar al’amurar Jihar Kaduna, tare da yin aiki tukuru wajen dawo da irin hadin kan da ake da shi a da, a tsakanin al’ummomin Jihar mabambanta addinai, da yare.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s