Kaduna 2023: IN AN ZABE NI GWAMNA, ZAN CI GABA DA KYAWAWAN KUDURORIN BALARABE MUSA

—– Hayatuddeen Makarfi

Dan takarar kujerar gwamnan Jihar Kaduna a karkashin tutar Jam’iyyar PRP, Alhaji Hayatuddeen Lawal Makarfi ya ce muddin al’amurar Jihar Kaduna su ka zabe shi a matsayin gwamnan Jihar, zai mayar da hankali ne wajen dorawa a kan kyawawan kudurori guda uku wanda tsohon gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Balarabe Musa ya soma a lokacin mulkin shi.

Alhaji Hayatuddeen Makarfi ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke gabatar da kundin kudurorin shi guda uku a cibiyar kungiyar’yan Jaridu NUJ reshen Jihar Kaduna wanda zai gudanar domin ciyar da Jihar Kaduna gaba, musamman tattalin arzikin Jihar ya bunkasa.

Hayatuddeen ya ce ayyukan da Balarabe Musa ya mayar da hankali su ne, farfado da masaku, Samar da ingantaccen wutar lantarki, sa’annan an San shi da fading gaskiya musamman a game da abin da ya shafi cin hanci da rashawa wanda ya zama abin damuwa.

kudurorin uku sun hada da farfado da tattalin arzikin Jihar Kaduna ta hanyar Samar da sabbin dabaru, sai na biyu yin adalci a tsakanin al’umma, sa’annan na uku shi ne gina al’umma su iya tsayawa da kafafafuwan su.

Dangane da abin da ya shafi ilimi kuwa, ya ce gwamnatin shi za ta ba da fifiko wajen samar da duk abubuwan da ake bukata na tafiyar da harkar karatu tare da samar da kwararrun malamai wadanda za su koyar da Yara su sami ingantaccen ilimi.

Har ila yau ya ce a bangaren harkar lafiya, aikin gona da samar wa matasa da mata ayyukan da za su dogara da kan su ta hanyar koyar da su sana’o’i iri daban dabam wanda zai kawar da su daga zaman kashe wando.

Da ya juya batun gurbacewar zamantakewa a tsakanin al’ummar Jihar Kaduna inda kiristoci da musulmai kowa na zaune ne a bangaren da ya fi samun natsuwa da kwanciyar hankali.

Ya nuna taikaicin shi a game da wannan hali da ake ciki inda ya ce musulmi bai sakin jiki da wanda ba musulmi ba, sa’annan wadanda ba musulmai ba, ba sa sakin jiki da musulmai.

Alhaji Hayatuddeen Makarfi ya ce a da duk bukukuwan Sallah da kirsimeti in lokacin ya yi, musulmai da kiristoci su na ziyarar juna, suna taya juna murna amma ya ce yanzu ba haka ba ne inda ya ce zai tabbatar da cudanya, yarda da son juna a tsakanin al’ummar Jihar Kaduna komi ya dawo kamar yadda ya ke a da.

Daga nan sai ya bukaci su ‘,Yan Jaridu su yi aikin su bisa tanadin dokokin tafiyar da aikin Jarida, su yi adalci ga kowa wajen tafiyar da aikin su wanda ya ce yana da mahimmanci a tsakanin al’umma.

Tun da farko a jawabin ta, shugabar kungiyar’yan Jaridu NUJ reshen Jihar Kaduna Hajiya Asma’u Yawo Halilu ta ce za su yi adalci ga kowane dan takara ta wajen yada manufofin shi ba tare da nuna fifiko ba ga wani.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s