—- Injiniya Kailani Mohammad
Jigo a hadakar kungiyoyi masu fafatukar yakin neman zaben shugaban kasa na APC (BCO), Injiniya Kailani Mohammad ya ce rahotannin da su ke samu a duk daukakin Jihohin kasar nan na yin nuni da cewa Jam’iyyar APC za ta sami fafi yawan zababbun Gwamnoni da ‘yan majalisun Jihohi a wannan zaben da ke gudana a yau.
Injiniya Kailani Mohammad ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai Jim kadan bayan da ya kada kuri’ar shi a akwatin zabe mai namba 054 da ke layin Abuja a Rigasa Kaduna.
Ya kara da cewa a mazabar A da B, a masarautar Jama’a wato Kafanchan, duk APC ne, haka a Sanga ya ce za su yi kankankan, haka a Kagarko zai kasance kamar haka.
Har ila ya ce a Kachiya APC ce za ta yi galaba, haka Lere, nan ya ce APC ne ballantana kuma a shiyya na tsakiya, da shiyya na daya yankin Zariya. nan ya ce APC ne za ta yi galaba babu tantama.
Injiniya Kailani ya yaba wa hukumar zabe INEC wanda ya ce tsarin da ta yi ya yi kyau komi na tafiya daidai, musamman yin amfani da na’urar BVAS babu matsala ko miskala zarratin.
Haka ya yaba wa Jami’an tsaro yadda suke gudanar da aikin su komi na tafiya bisa tsarin tsaro bubu mishkila.
A nada tsokacin, Hajiya Farida na Gamayyar Kungiyoyin yakin neman zaben shugaban kasa BCO, ta ce ta gamsu da yadda zaben ke tafiya a Jihar Kaduna inda su ka zo suke sa Ido.
Ta kara da cewa sun zagaya rumfunan zabe guda ashirin kenan har da wannan rumfar zabe mai namba 054 a layin Abuja inda Injiniya Kailani Mohammad ya kada kuri’ar shi.
Hajiya Farida ta yaba wa Jami’an tsaro yadda suke gudanar da aikin su cikin tsari babu inda aka sami rahotannin tashin hankali, haka ma ta yaba wa hukumar zabe INEC saboda kai kayayyakin zabe cikin lokaci wanda ya ba da dama aka fara yin zaben cikin lokaci.
Shi ko mai girma Sarkin Sabon Garin Rigasa, Alhaji Muhammadu Jibrin, ya yaba da yadda hukumar zabe INEC ta yi shiri cikin tsari inda ta raba kayayyakin zabe cikin lokaci wanda ya ba da dama aka fara yin zaben cikin lokaci.
Alhaji Muhammad Jibrin haka ya yaba wa jami’an tsaro bisa yadda suka jajirce suke sa ido a duk rumfunan da ya zagaya komi na tafiya daidai babu tashin hankali ko kadan.
Sarkin Sabon Garin Rigasa hat ila yau ya yaba wa al’amurar sa wadanda su ka fito kwansu da kwakkwarar su inda suka gudanar da zaben su cikin tsari da kwanciyar hankali da lumana.