Madrasatul Riyadul Qur’An Lizzakariya’u : IN KUN SANYA TSORON ALLAH A KARATUN KU DA AYYUKAN KU ALLAH ZAI ALBARKACI RAYUWAR KU

— CP Sheikh Abdul-Rahman.

Daga Balarabe Junaidu Nuhu, Kaduna .

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kaduna CP Ahmad Abdul-Rahman ya jawo hankalin dalibai masu saukar haddar Al-Kur’Ani na makarantar Madarasatul Riyadul Kur’An Lizzakariya’u dake” Sardauna Cresent ” kaduna da cewa su sa tsoron Allah da kuma sanya karatun da suka yi na haddar Al-Kur’Ani a cikin ayyukan su sai Allah ya albarkaci rayuwar su.

Kwamiahinan ‘yan sandan CP Sheikh Ahmad Abdul-Rahman ya yi wannan kiran ne a sakon shi ta hannun wakilin sa, babban Limamin hedkwatar rundunan ‘yan sandan, DSP Khalid Wada Khalid a matsayin shi 1na shugaban taro a wurin bikin yaye dalibai na makarantar Madarasatul Riyadul Kur’An Lizzakariya’u a Kaduna wanda ya gudana a dakin taro na gidan Arewa a karahen makon jiya.

Ya kuma gargade su da cewa ” Ka da ku kasance kun yi haddar Al-Kur’Ani amma maimakon yin aiki da shi sai ku rungumi wani abu daban wanda da karantarwan Al-Kur’Ani ba wannan ba daidai bane, ” Inji shi.

Haka ya ce yana taya su murna da farin ciki tare da sanya masu albarka.

Sannan ya nuna godiya ga iyaye da malamai wadanda suka yi aiki tukuru wajen ba wadannan dalibai mahaddata tarbiyya wanda ya kai su ga wannan mataki a yau.

CP Sheikh Ahmad Andul-Rahman sa’annan sai ya mika godiya ga manyan bakiin da su ka halarci bikin yaye dalibai mahaddatan tare da fatan kowa ya isa gida lafiya.

A nashi jawabin,shugaban makarantar Ustaz Idris Abdullahi El-Salti ya ce sun kafa wannan makarantan ne a shelarar 2007 .

Ya ce makasudin assasa wannan makaranta shi ne akan abu uku,” Na farko ka fahimci iya karatun Al-Kur’Ani da Larabci, kuma ka kasance kana da wayewa na zamani,ya lasamce damar ka da hagun ka lomai daidai.”

Haka ya ce tun kafa makarantar sun yaye dalibai masu sauka da mahassatan Al-Kur’Ani kimanin su 200 , kima suna da kwararrun malamai wadanda su ka sadaukar da wani bangare na lokacin su suke zuwa suna koyarwa ba don kudi ba amma saboda su ba da nasu gudun mawa ta wajen gina addinin Allah.

Ya ce makarantar tana da sassa hudu ne, a kwai mutawassid,sanawiyya,Islamiyya,da Tahfiz,dukkanin wadannan sassa sun yaye dalibai wasu na kasashen waje irin su Sudan da Misira kuma yace suna basu kwarin guiwa su tsaya su yi karatun.

Haka ya ce daga cikin daliban wannan makarantan a kwai Lokitoci, Injiniyoyi da masu digiri da HND a sassa daban dabam wanda suna alfahari a kan wannan ni’imar da Allah ya yi masu a wannan makaranta mai albarka .

Leave a comment