2019 : KU BUDE IDANUWAN KU DA KYAU KU ZABI SHUGABANNI NA KWARAI MASU MUTUNCI

—— Ramlat Isah Ashiru

Daga Balarabe Junaidu Nuhu, Kaduma .

Uwargidan dan takaran kujerar gwamna a karkashin tutar jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna,Hajiya Ramlat Isah Mohamed Ashiru Kudan,ta bukaci al’ummar Jihar Kaduna musamman mata da matasa da su bude idanuwan su da kyau a lokacin zabe su zabi shugabanni na kwarai masu mutunci .

Hajiya Ramlat Isah Ashiru ta yi wannan kiran ne a cikin sakon da ta aike ta hannun wakilin ta Mustapha Idris na gidan Tallabijin na DITV a wurin bikin saukar dalibai mahaddata na makarantar Madarasatul Riyadul Kur’An Lizzakariya’u wanda ya gudana a karshen mako, a dakin taro na gidan Arewa a Kaduna .

Ta ce yin kiran ya zama dole ganin zabe ya zo dab kuma ‘yan siyasa sun dukufa sosai wajen yin kamfen domin neman kuri’un jama’a.

Haka ta ce masu zabe kada su yi gaggawa a kan yanke hukunci dan takaran da za su zaba sai sun duba sun tanyance sun ware na kwarai.

Ta ce jiki magayi kowa ya dandana irin halin da ake ciki don haka a yi karatun ta natsu a raba Aya da Tsakuwa .

Hajiya Ramlat Isah Ashiru sanman sai ta bukaci mata da marasa a kan su tabbatar da sun mallaki katunan zaben su PVC”s wanda da su ne za su iya zaben wanda ya kwanta masu a rai.

Da ta jiya kan dalibai masu saukar haddar Al-Kur’Ani mai tsarki kuwa, ta taya su murna tare da yin kira an gare su da si yi amfani da wannan karatun da Allah ya azurta su d an shi su kyautata dangantakar su da Allah domin su sami albarka mai tarin yawa .

Haka ta yaba wa iyaye da malamai a kan kyakkyawar tarbiyyar da su ka ba daliban , sa’annan kuma ta ba da gudunmawar kudi har N50,000 fisabillah .

Leave a comment