Kai Hare-Hare A Jihar Kaduna : MAJALISAR SARAKUNAN AREWA TA YI ALLAH WADAI DA LAMARIN INDA TA CE, WANNAN HAUKA NE, WAJIBI NE A KAWO KARSHEN SHI

Daga Balarabe Junaidu Nuhu, Kaduna .

Kwamitin Gudanarwan Majalisar Sarakunan Arewa, sun gudanar da taro na musamman, a yau Litini 7 ga watan Satumba , 2020 inda su ka ce, rigingimun da ke faruwa a sassa daban dabam na yankin kudancin Jihar Kaduna wanda ya ke haifar da kashe kashen rayuka tare da barnata dukiyoyin al’ummar da abin ya shafa, aiki ne na hauka wanda dole ne a matsayin su na Shugabanin al’umma a hada karfi da karfe tare da bangaren gwamnati domin a kawo karshen shi .

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar Sarakunan Arewa , Alhaji Sa’ad Abubakar Na lll, shi ne ya sanar da hakan a cikin jawabin shi da ya gabatar a wurin taron, a matsayin shi na mai masaukin baki .

Daga nan sai ya ce ” muna jajanta ma gwamnatin Jihar Kaduna tare da al’ummar Jihar baki daya a game da wannan lamari sannan da yardar Allah mu sarakuna za mu yi iyakan mu, mu samo hanya mafita wanda za a kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa, a sami fahimtar juna, zaman lafiya ya tabbata .

Mai alfarma Sarkin Musulmin har ila yau ya ce, yawancin kai hare haren bai da nasaba da addini ko kadan amma wadanda ke kitsa rikicin suna rabewa ne da addini domin su cimma biyan bukatun su, musamman a siyasance inda ya gargadi da cewa duk abin da mutum ya shuka zai tsaya gaban ubangiji Allah ya amsa tambayoyi .

Daga nan sai ya jawo hankalin mahalarta taron wato, sarakuna ‘yan uwan shi da cewa duk irin abubuwan da suka tattauna suka zartar, kowa ya rike amana ya tsaya a kan matsayin da suka imma, ba ragi, ba kari domin a cimma nasarar abin da ake da kuduri a Kai shi ne, a sami dauwamamnen zaman lafiya tare da fahimtar juna .

Ya tabbatar wa gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i da cewa a karshen taron za su fitar da matsayar su kuma za su tura mashi donin ya duba, ya yi nazari kuma da yardar Allah komi zai daidai ta batun kawo ire iren wannan tashe tashen hankali, ba ma a Jihar Kaduna ba Kai, har sauran jihohin da suke fuskantar irn wadannan matsalolin a yankin Arewa da kasa baki daya .

Haka ya ce taron zai duba batun cutar korona birus wanda ya shafi duk harkokin al’ummar yau da kullum, na rayuwa, da tafiyar da al’ummar gwambati .

Mai alfarma Sa’ad Abubakar Na lll, ya yaba da gudunmawar wasu Shugabanin addininai na musulunci, da kiristanci wadanda suka ziyarci fadar gwamnatin Jihar Kaduna kuma suka gabatar da jawabai masu tasiri wadanda za su taimaka wa gwamnati a sami dauwamamnen zaman lafiya .

A nashi jawabin, gwamna Mallam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya mika godiya na musamman da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar wanda ya kawo ziyara na musamman inda ya jajanta ma gwamnatin a game da abubuwan da ke faruwa, sannan ya kara ba gwambati kwarin guiwa inda aka shirya wannan muhimmin taro domin nemo mafita ta yadda za a kawo karshen wannan matsalolin a Jihar Kaduna da ma sauran sassar jihohin Arewacin kasar .

Gwamna Nasir El-Rufa’i har ila yau ya ce ” Jihar Kaduna a kwai jinsin kabilu daban dabam har guda 5o, sannan a kasar gabadaya akwai jinsin kabilu kimanin 585, kashi 10 daga cikin wadannan junsunan kabilun sana zaune ne a wata jiha a Nijeriya, wannan Jihar kuwa ita ce Jihar Kaduna saboda kasancewar ta wata karamar Nijeriya ce domin duk jinsin kabilun da ke kasar suna zaune a Jihar Kaduna,” inji shi .

Daga nan sai ya koka a kan cewa yawancin in rikici ya faru wasu sukan juya shi su msyar da shi wala na addini ko na kabilanci wanda tun fil azal batun ba haka ba ne .

Ya ce wannan kadan kenan daga kalubalen da suke fuskanta a jihar wanda ya ce ta Sha bambam da sauran jihohin da suke fuskantar matsala makamancin haka inda ya ce, yawancin su kusan jinsi daya ne kuma addini daya .

Daga nan sai ya bukaci taron da ya duba ya samo hanyoyin da za a kawo karshen wannan matsalolin hare-hare, satar mutane da yin garkuwa da su, da satar shanu ta hanyar yin amfani da hikimar da Allah ya ba su na, sarakuna, Shugabanin al’umma ta wajen fadakar da su a kan irin muna an abubuwan da su ke aikatawa .

Ya jaddada cewa duk irin shawar da suka zartar, gwamnatin Jihar Kaduna za ta tabbatar da an aiwatar domin kyautata zamantakewa da inganta rayiwar al’ummar Jihar baki daya .

Leave a comment