PDP A JIHAR KADUNA, TA BAYYANA RASUWAR MAI MARTABA SARKIN ZAZZAU, ALHAJI SHEHU IDRIS A MATSAYIN BABBAR RASHI NE GA KASA

—- Hassan Hyat

Daga Balarabe Junaidu Nuhu, Kaduna .

Sabon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, Honorabul Hassan Hyat, a madadin ‘ya’yan jam’iyyar PDP, ya bayyana rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris a matsayin babbar Rashi ga kasa .

Honourabul Hassan Hyat, ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a jiya jim kadan, bayan an mika masu ragamar mulki a yayin kammala zabubbuka da aka gudanar, a Jihar .

Ya bayyana shi a matsayin shugaban da aka fi girmamawa a jerin Sarakunan kasar nan saboda saukin kan shi da kokarin shi na karfafa zaman lafiya a tsakanin kabilu daban dabam, da addinai daban daban da ke masarautar da, da Jihar Kaduna, da kasa baki daya .

Shugaban jam’iyyar PDP din har ila yau, ya bukaci duk wanda Allah ya ba da ya yi koyi da irin salon shugabancin shi na adalci da karfafa hadin kai a tsakanin al’ummori daban dabam .

Dangane da wadanda suka yi takara da si, suka fadi, ya ce yana kira da su so a yi aiki tare domin karfafa jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna saboda su tabbatar da ceto al’ummar Jihar Kaduna daga mulkin APA, wanda ya abin takaici ne irin abubuwan da ke faruwa a kasa, na rashin tsaro, da kuntatar rayuwa ga talakawan jihar, da kasa baki .

Hassan Hyat, ya jinjina wa wakilan kwamitin da suka gudanar da zabubbukan wanda ya ce, an yi shi bisa ka’ida ta yadda kowa ya gamsu .

Shi ma sakataren jam’iyyar, Honorabul Wusono, a madadin dukkan zababbun, na mika godiya ga daukakin wakilan da suka zabe su, da sauran ‘ya’yan jam’iyyar PDP da suka tsaya suka ga an gudanar da zabubbukan cikin kwanciyar hankali.

A nashi jawabin, shugaban riko na jam’iyyar PDP, a Jihar Kaduna, Honorabul Bashir Dutsen-Ma, ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar PDP din da su ba Sababbin shugabannin jam’iyyar goyon baya saboda ciyar da jam’iyyar gaba .

Leave a comment